Kenya: An Kama Mutane 6 Da Ake Zargi Da Ta'addanci.
'Yan sandan Kenya sun kame mutane 6 a yankin Malinda da ke kudu maso gabacin kasar.
'Yan sandan Kenya sun kame mutane 6 a yankin Malinda da ke kudu maso gabacin kasar.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinuha na kasar Sin, ya ambato majiyar tsaron kasar ta Kenya na cewa; Mutanen da aka kama suna da alaka ne kai tsaye da kungiyare al-shabab kuma suna samun kudade daga gare ta.
Rahoton ya ci gaba da cewa; A cikin wayoyin tafi da gidanka na mutane an sami bayanai na musayar kudade a tsakaninsu da kungiyar al-shabab.
Kasar Kenya dai tana fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyar ta al-shabab ta kasar Somaliya.
A baya kungiyar ta kai munanan hare-hare a cikin kasar ta Kenya da ya haddasa mutuwar mutane da dama.