Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zanga A Mauritania
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18440-dubban_mutane_sun_yi_zanga_zanga_a_mauritania
Kawancen jam'iyyun adawa na FNDU a Mauritania ya bukaci majalisar datijan kasar data yi watsi da shirin gwamnatin kasar na yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
(last modified 2018-08-22T06:59:48+00:00 )
Mar 12, 2017 02:20 UTC
  • Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zanga A Mauritania

Kawancen jam'iyyun adawa na FNDU a Mauritania ya bukaci majalisar datijan kasar data yi watsi da shirin gwamnatin kasar na yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Dubban magoya bayan kawancen ne suka gudanar da wata zanga-zanga jiya Asabar inda sukayi kira ga majalisar da kada ta amunce da wannan shirin.

A gobe Litinin ake sa ran majalisar datijan kasar zata duba bukatar gwamnatin na yiwa kudin tsarin mulkin gyaran fuska bayan da majalisar dokokin kasar ta amunce da hakan da gagarimun rinjaye a ranar Alhamis data gabata.

Gwamnmatin shugaban Mohamed Ould Abdel Aziz dai na son a kawo sauyi a kundin tsarin mulkin kasar da ake aiki dashi tun cikin shekara 1991.

Sauye sauyen da gwamnatin ke son kawowa sun hada da soke wasu hukumomi da suka hada da majalisar datijai da kotun koli da majalisar koli ta addinin Islama, da kuma mukamin mai shiga tsakani na gwamnati, da canza tutar kasar.