An Yi Zanga-zanga Kan Tsadar Man Fetur A Togo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18466-an_yi_zanga_zanga_kan_tsadar_man_fetur_a_togo
A kasar Togo dubun dubbatar mutane ne suka gudanar da wata zanga zanga a Lome babban birnin kasar kan karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 12, 2017 14:18 UTC
  • Zanga zanga tsadar man fetur a birnin Lome na Togo.  HOTO : GETTY IMAGE
    Zanga zanga tsadar man fetur a birnin Lome na Togo. HOTO : GETTY IMAGE

A kasar Togo dubun dubbatar mutane ne suka gudanar da wata zanga zanga a Lome babban birnin kasar kan karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.

Masu zanga-zanga dai na bukatar a rage farashin man da ya yi tashin gobron zabo sakamakon karin kashin 10% da gwamnatin kasar tayi.

Wannan karin dai shi ne na biyu da akayi akan farashin man fetur a kasar a kasa da wata guda.

Shugaban kungiyar masu amfani da kayayaki na yau da kulin a kasar ta Togo ya ce wannan canje-canje da ake samu na farashin mai na tasiri a aljifun talaka, wannan ya danganta da rashin tausayi na mahukuntan kasar, musamen akan wahalhalun da jama'a ke fama dasu.

A nasu bangare 'yan adawa a kasar da suka shirya zanga zanga ta jiya Asabar sun bukaci gwamnati data soke karin kudin man.

Gwamnatin kasar dai na danganta karin farashin man da karin kudin ganganr mai a kasuwannin duniya wanda ya kama daga Dala 38,38 a watan Janairu na shekara data gabata zuwa $ 55 a watan Janairu na wannan shekara.