Habasha : Zabtarewar Kasa Ta Kashe Mutane 46
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18468-habasha_zabtarewar_kasa_ta_kashe_mutane_46
Rahotannin daga Habasha na cewa akalla mutane 46 ne suka rasa rayukansu, kana wasu da dama suka jikkata sakamakon zabtarewar kasa data auku a wani wuri dake kewayen Addis Ababa baban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:48+00:00 )
Mar 12, 2017 14:28 UTC
  • Babu bayyani akan abunda ya hadasa wannan iftila'in. HOTO AFP
    Babu bayyani akan abunda ya hadasa wannan iftila'in. HOTO AFP

Rahotannin daga Habasha na cewa akalla mutane 46 ne suka rasa rayukansu, kana wasu da dama suka jikkata sakamakon zabtarewar kasa data auku a wani wuri dake kewayen Addis Ababa baban birnin kasar.

Yankin da lamarin ya auku ya kasance wani babban jubji dake da fadin Hecta 30 inda ake zub da shara a wajen babban birnin kasar, inda kuma al'ummar dake rayiwa wurin ke sintar wasu kayayaki da ake iya sake sarafawa.

Kamfanin dilancin labaran faransa AFP ya rawaito cewa akasarin wadanda abin ya shafa marasa galihune da ke rayuwa a kusa da jibjin dake kudu maso yammacin birnin.

kawo yanzu babu bayyani akan abunda ya hadasa wannan iftila'in, saidai mazauna yankin na dangantasa da aikin da akeyi na fadada wani gefe dake kusan wurin zubda shara.

Yankin Koshe inda lamarin ya auku, ya kasance baban juji a Addis Ababa sama da shekaru 40, kuma akwai mutane kusan miliyan 4 da ke rayuwa a yankin.