Wata Mota Ta Tarwatse A Birnin Mogadishu Fadar Mulkin Kasar Somaliya
Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wani otel a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a safiyar yau Litinin.
Majiyar 'yan sanda a birnin Mogadishu ta bayyana cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wani otel da mutane ke yawan kai komo a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar a safiyar yau Litinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla biyu tare da jikkatan wasu uku na daban.
Majiyar ta kara da cewa: tarwatsewar motar bata janyo illa ga otel din ba, sai dai ta lalata wasu gine-gine da suke makobtaka da inda motar da tarwatse. Kuma har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma dai ana nuna yatsar zargin kan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab dake kasar.