An Sace Ma'aikatan Wata Cibiyar Amurka A Sudan Ta Kudu
Mar 13, 2017 19:25 UTC
Wasu masu dauke da makamai sun sace wasu ma'aikata 8 na wata cibiyar bayar da agaji ta Amurka a cikin kasar Sudan ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a yau ne gungun mutanen masu dauke da makamai suka kai farmaki kan ma'aikatan cibiyar, suka yi awon gaba da 8 daga cikinsu wadanda dukkanin 'yan kasar Sudan ta kudu ne.
Jim kadan bayan sace mutanen sun sanar da cewa suna garkuwa ne da ma'aikatan, kuma za su sake su ne kawai bisa sharadin bayar da kudaden fansa.
Kasar Sudan ta kudu dai tana fama da matsaloli na tsaro tun daga karshen shekara ta 2013, bayan da shugaban kasar ya kori mataimakinsa Reick Machar, wanda shi kuma ya shelanta tawaye.
Tags