Sojojin Gwamnatin Somaliya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana
Sojojin gwamnatin Somaliya sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.
Sojojin gwamnatin na Somaliya sun gudanar da zanga-zangar ce a jiya Litinin domin jaddada bukatarsu ta ganin gwamnatin kasar ta biya su hakkinsu na albashi na tsawon watanni goma sha biyu, inda sojojin suka dauki matakin toshe manyan hanyoyin zirga-zurgar motoci da shiga babbar kasuwar birnin a matsayin bayyana rashin jin dadinsu kan irin mummunan halin da suka shiga sakamakon rashin albashi.
Sojojin kasar ta Somaliya sun bukaci sabon shugaban kasar Muhammad Abdullahi Muhammad da ya dauki matakin tsoma baki domin ganin ya yantar da su daga mummunar kangin da suka shiga na rayuwa saboda rashin albashi.