Ana Zaman Makoki Na Kwanaki Uku A Habasha
-
Hukumomi sun sha gargadin mazauna yankin su bar wurin su koma inda aka kebe masu. HOTO : REUTERS
Majalisar dokoki a Habasha ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku, domin yuyayin mutanen da suka rasa rayukansu a zabtarewa kasa a wajen Adis Ababa babban birnin kasar.
A ranar Asabar data gabata ne aka fuskanci zabtarewar kasa a wurin dake kewayen birnin Adis Ababa wanda wani babban jubji inda al'ummar dake rayiwa wurin ke sintar wasu kayayaki da ake iya sake sarafawa.
Sabbin al'kalumen da mahukuntan kasar suka fitar sun ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 72, a yayin da kuma ake ci gaba da fargarbar adaddin zai karu.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da aikin ceto da zumar ko za'a samu wasu masu sauren rai na gaba.
Har kawo yanzu babu bayyani akan abunda ya hadasa wannan iftila'in, saidai mazauna yankin na danganatasa da aikin da akeyi na fadada wani gefe dake kusan wurin zubda shara.
Fira ministan kasar dai ya sha alwashin gudanar da bincike domin sanin hakikanin abunda ya faru.