Kenya : Likitoci Sun Dakatar Da Yajin Aiki
-
Shugaba Uhuru Kenyata na Kenya
Gwamnati da wakilan kungiyoyin likitoci a Kenya sun cimma wata yarjejeniya, wace ta kai ga dage yajin aikin da likitocin suka kwashe kusan kwanaki 100 sunayi a kasar.
Sakatare janar na kungiyar likitocin ce (KMPDU) Ouma Oluga ya bayyana a wannan rana cewa sun cimma matsaya ta komawa bakin aiki da gwamnati, wace ta kawo karshen yakin aiki daya tabarbare harkokin kiwan lafiya a kasar.
Babu dai karin bayyani akan matsayar da bangarorin biyu suka cimma, saidai a cen baya likitocin na nema ga gwamnati data yi musu karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu ciki har da samar da ingantatun kayan aiki a asibitocin gwamnati.
A cen baya dai gwamnatin kasar ta sha yiwa likitocin barazana ta korarsu daga bakin aiki domin cilasta masu komawa bakin aiki.
A cikin shekara 2013 ne gwamnati da kungiyar likitocin suka cimma wata matsaya ta shafe masu hawaye saidai tun lokacin gwamnati bata sake waiwayensu ba, lamarin daya cilasta masu tsunduma yajin aiki domin cimma bukatunsu.