Kokarin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18550-kokarin_kafa_gwamnatin_hadin_kan_kasa_a_sudan
Mataimakin shugaban kasa kuma fira ministan kasar Sudan ya jaddada cewa: Bayan kammala gudanar da shawarwari da dukkanin bangarorin da abin ya shafa zasu hanzarta kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan.
(last modified 2018-08-22T06:59:49+00:00 )
Mar 16, 2017 03:26 UTC
  • Kokarin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Sudan

Mataimakin shugaban kasa kuma fira ministan kasar Sudan ya jaddada cewa: Bayan kammala gudanar da shawarwari da dukkanin bangarorin da abin ya shafa zasu hanzarta kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan.

A ziyarar aikin da ya kai lardin Aljazirah da ke tsakiyar kasar Sudan a jiya Laraba: Mataimakin shugaban kasa kuma fira ministan kasar Sudan Bakri Hassan Saleh ya yi furuci da cewa: Gwamnatin Sudan tana goyon bayan shirin kafa gwamnatin hadin kan kasa da nufin samar da zaman lafiya da sulhu a yankunan kasar da suke fama da matsalolin tashe-tashen hankula.

Bakri Hassan Saleh ya kara da cewa kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan zai taimaka wajen kara samun hadin kan al'ummar kasar tare da wanzar da zaman lafiya da sulhu da nufin fuskantar matsalolin da suke ci gaba da addabar kasar ta Sudan a bangarorin da dama.

Har ila yau mataimakin shugaban kasar ta Sudan ya sake jaddada yin kira ga jam'iyyun adawa da kungiyoyin 'yan tawayen kasar da suka bijirewa zaman taron kasa da su janye wannan ra'ayin nasu domin kawo gudumawarsu a fagen habaka ci gaban kasar ta Sudan.