Ahmad Na Madagasca Ya Zama Sabon Shugaban CAF
Mar 16, 2017 10:29 UTC
-
Sabon shugaban hukumar CAF, Ahmad. HOTO : AFP
An zabi, Ahmad Ahmad, na kungiyar kwallon kafar Madagasca, a matsayin sabon shugaban hukumar kwallo kafa ta Afirka (CAF).
Mista Ahmad dan shekaru dan shekaru 57 ya dau wannan matsayin ne bayan ya kada Isa Hayatu na Kamaru a zaben da aka gudanar yau Alhamis a birnin Adis Ababa na Habasha.
Hayatu dan shekaru 70 ya shugabanci hukumar na kusan tsawan shekaru 29, kuma a ko wanne lokaci baya samun abokin hammaya.
Wakillan kasashe membobin hukumar sun zabi Ahmad da kuri'u 34, yayin da Hayatu ya samu guda 20.
Ahmad ya zama shugaban hukumar ta CAF na bakwai tun bayan kafa ta a shekaru 60 da suka gabata.
Tags