An kai wa tawagar kai Agajin gaggawa hari a Sudan ta Kudu
Wani gungun 'yan bindiga sun kai hari kan tawagar kungiyar kai agajin gaggawa a kasar Sudan ta Kudu.
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a wannan Alkhamis cewa wani gungun 'yan bindiga sun kai hari kan tawagar kai agajin gaggauna na Majalisar a kasar Sudan ta kudu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane biyu tare da jikkatar wasu uku na daban.
Hukumar ta kasar da cewa bayan harin da 'yan bindigar suka kai kan ma'aikatan kai Agajin, maharan sun yi awan gaba da kayan agajin da za a kaiwa mutanan dake sansanin 'yan gudun hijra.
A watan da ya gabata Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa wani bangare na kasar Sudan ta kudu ya fuskanci karamcin ruwan sama , domin haka kimanin rabin Al'ummar kasar da adadin su ya kai kimanin Miliyar biyar za su fuskanci matsalar karamcin abinci, wanda hakan ne ma ya sanya Majalisar daukan matakan gaggauwa na kai agaji cikin kasar.
Baya ga wannan matsala ta fari, tun daga shekarar 2013 ne kasar take fuskantar yakin cikin gida tsakanin Sojojin dake biyayya da Shugaba Salva keiir da kuma wadanda suke biyayya da tsohon mataimakin shugaban kasa kum madugun 'yan tawaye Riek Machar.