An hallaka Komandan kungiyar Ashabab a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18568-an_hallaka_komandan_kungiyar_ashabab_a_somaliya
Wani babban Jami'in tsaron kasar Somaliya ya sanar da hallaka daya daga cikin manyan komondoijin kungiyar Ashabab a Magadushu babban birnin Kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:49+00:00 )
Mar 16, 2017 14:32 UTC
  • An hallaka Komandan kungiyar Ashabab a Somaliya

Wani babban Jami'in tsaron kasar Somaliya ya sanar da hallaka daya daga cikin manyan komondoijin kungiyar Ashabab a Magadushu babban birnin Kasar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abdulfatah Halatah daya daga manyan Jami'an tsaron Somaliya ya ce a  farmaki da Jami'an tsaron kasar ke kaiwa kan mayakan mayakan Ashabab, sun samu nasarar gano Ja'afar Kukai daya daga cikin manyan Komandojin Kungiyar ta'addancin ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida a anguwar Haliwa na birnin Magadushu fadar milkin kasar.

Abdulfatah Halatah ya kara da cewa a yayin kai farmakin Dakarun tsaro sun gano  tare da kame makamai gami da harshashe masu yawa a maboyar Ja'afar Kukai daya daga cikin manyan Komandojin Kungiyar ta Ashabab.kasar Somaliya dai ta kwashe shekaru da dama tana fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Ashabab.

A shekarar 2012 ne Kungiyar ta Ashabab ta hade da kungiyar Alka'ida, a baya dai kungiyar ta mamaye wani bangare na kudu da tsakiyar kasar , amma a shekarar 2015, bayan shigar Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka an fatattaki mayakan kungiyar a manya-manyan buranan kasar.a halin da ake cikin abinda ya rage a hanun kungiyar bai fice wasu kananan kauyuka ba a kudancin kasar.