Mauritaniya : Sanatoci Sun Yi Watsi Da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima
Mar 18, 2017 02:24 UTC
Majalisar dattijan Mauritaniya ta yi watsi da shirin gwamnati na bukatar a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
'Yan majalisa 33 ne daga cikin 56 da majalisar ta kunsa ne suka yi watsi da bukatar gwamnatin.
Wannan dai na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta amunce da shirin a zamenta na ranar 9 ga watan Maris.
Shirin dai na bukatar amuncewa da kashi biyu cikin uku na dukkan majalisun biyu kafin ya samu karbuwa.
Sauye sauyen da gwamnatin ke bukatar kawowa sun hada da soke wasu hukumomi da suka hada da majalisar dattijan kan ta, da kotun koli da majalisar koli ta addinin Islama, da kuma mukamin mai shiga tsakani na gwamnati, da canza tutar kasar.
Tags