Karfafa Sulhu da inganta rayuwa shi ne manufar Taron kungiyar IGAD
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18610-karfafa_sulhu_da_inganta_rayuwa_shi_ne_manufar_taron_kungiyar_igad
'Yan Majalisun kasashen dake cikin Kungiyar IGAD suna gudanar da taron gwanaki biyu da nufin karfafa sulhu a yanki tare da kuma duba hanyoyin kiyaye canjin yanayi gami da kalubalantar hijrar da Matasan yankin ke yi zuwa kasashen Turai ba kan ka'ida ba.
(last modified 2018-08-22T06:59:50+00:00 )
Mar 18, 2017 02:33 UTC
  • Karfafa Sulhu  da inganta rayuwa shi ne manufar Taron kungiyar IGAD

'Yan Majalisun kasashen dake cikin Kungiyar IGAD suna gudanar da taron gwanaki biyu da nufin karfafa sulhu a yanki tare da kuma duba hanyoyin kiyaye canjin yanayi gami da kalubalantar hijrar da Matasan yankin ke yi zuwa kasashen Turai ba kan ka'ida ba.

Mohamed Adam Mohamed Ismail Shugaban kungiyar Bunkasa tattalin arzikin gabashin Afirka IGAD ya bayyana cewa manufar taron kungiyar na kwanakin biyu shi ne binciko hanyar kalubalantar canjin yanayi da kuma yaki da hijrar 'Matasan yankin zuwa Turai ba a kan ka'ida ba gami da lalubo hanyar tabbatar da Sulhu a yankin.baya ga wannan Shugaban ya yi ishara da mumunar dabi'ar sare itace na fitar hanakali a kasashen Sudan ta kudu da Ethiopia gami da asarar rayukan matasan yankin dake kokarin zuwa Turai a tekun Bahrum, inda ya tabbatar da cewa wadannan matsalolin guda uku na daga mahiman batutuwan da taron zai tattauna a kan su.

Mahalarta taron sun bukaci taimakon gaggawa ga kasashen yankin da suke fuskantar matsalar karamcin abinci sanadiyar fari, taron ya zo a daidai lokacin da dama daga cikin kasashen gabashin Afirka ke fuskantar matsalar fari, yakin basasa gami da hare-haren ta'addanci da kawo cikas game da tsaro gami da konciyar hankali na yankin.

Canjin yanayi na daga cikin dalilan da suka aifar da matsalar karamcin abinci a yankin kuma hakan ya biyo bayan sakamakon aiyukan manyan kamfanonin kasashen Yamma da suke gurbatar da yanayi a kasashen Afirka, baya ga wannan matsala,  ambaliyar ruwan sama ya tafi da mafi yawan amfanin gonaki a wasu sassa da dama na yankin Afirka,a bangare guda kuma wasu yankunan ba su samu saukar ruwan saman ba.

A halin yanzu mazauna yankuna da dama na kasashen Somaliya, Habasha da Sudan ta kudu na cikin wani mawuyacin hali na rmusifar yunwa, duk da cewa kamfanonin kasashen yamma ne umar aba'isar wannan matsala, da kuma ya kamata su biya diya kan wannan bala'i da suka janyo wa Al'umma, to saidai babu wani abin a zo a gani da ksashen na Yamma suka yi dangane da taimakawa Al'ummar yankin.

A bangare guda, hare-haren ta'addanci da kungiyar Ashabab ke ci gaba da kaiwa a kasar Somaliya ya janyo babban cikas ga harakokin tsaron kasar, mafi yawa daga cikin kasafin kudin kasar na tafiya ne a bangaren harakokin tsaro ta yadda za a samu damar siyan makamai na zamani domin kalubalantar mayakan kungiyar ta Ashabab.A cikin irin wannan yanayi, talauci da rashin aikin yi ya karu a kasashen yankin gabashin Afirka, lamarin da ya sanya matasan yakin ke hijra zuwa kasashen Turai domin neman abin za taimakawa kansu da kuma iyalan su.

Haka zalika a bangare kasar Sudan ta kudu, Yakin basasar da ya ki ci yaki cinyewa tsakanin magoya bayan Shugaban kasar Salva Keir da kuma bangaren Riek Machar tsohon mataimakin Shugaban kasar na farko kuma madugun 'yan tawaye ya janyo babban cikas ga zaman lafiyar kasar, su kuma Mutanan kasar Habasha mafi yawansu su nuna rashin amincewar su da yadda Gwamnatin kasar ke gudanar da milkin kasar.

Tabbatar da tsaro, kyautata rayuwar Al'umma, hana matasan kasar yin hijra zuwa kasashen Turai da kuma sake gina kasashen yankin na daga cikin mahiman batutuwan da mahalarta taron kungiyar IGAD din suka sanya a gaba inda manazarta ke ganin cewa, matukar dai suka dauki matakin baiwa daya zai taimaka wajen magance wasu matsalolin da yankin ke fama da shi.