An Kame Wani Bayahuden Isra'ila Kan Zargin Leken Asiri A Kasar Masar
Jami'an tsaron Masar sun kame wani dan haramtacciyar kasar Isra'ila kan zargin gudanar da ayyukan leken asiri a yankin Ahram na kasar ta Masar.
Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame wani dan yawon shakatawa mai dauke da izinin zaman kasashen Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila kan zargin gudanar da ayyukan leken asiri a yankin Ahram mai tsawon tarihi na kasar ta Masar.
Majiyar ta kara da cewa: Jami'an tsaron kasar Masar sun kame mutumin ne yana amfani da jirgin sama maras matuki ciki wajen daukan hotuna a yankin na Ahram, kuma tuni suka mika shi ga bangaren shari'a domin gudanar da bincike kansa. A nashi bangaren dan yawon shakatawar ya gabatar da kansa a matsayin mai shirya fila-filan sinima tare da da'awar cewa baya da masaniyar doka ta hana amfani da jirgin sama maras matuki ciki wajen daukan hotuna a wajajen tarihi na Ahram.