Somalia ta bukaci a binciki kisan 'yan gudun hijiranta a Teku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18658-somalia_ta_bukaci_a_binciki_kisan_'yan_gudun_hijiranta_a_teku
kasar Somalia ta bukaci Saudiya da ta gudanar da bincike kan kisan ‘yan gudun hijiran kasar da aka aikata a kan teku.
(last modified 2018-08-22T06:59:50+00:00 )
Mar 20, 2017 02:25 UTC
  • Somalia ta bukaci a binciki kisan 'yan gudun hijiranta a Teku

kasar Somalia ta bukaci Saudiya da ta gudanar da bincike kan kisan ‘yan gudun hijiran kasar da aka aikata a kan teku.

Ya zuwa  yanzu dai babu wani cikakken bayani da aka fitar dangane  maharan da suka kashe ‘yan gudun hijira sama da 40 a cikin jirgin ruwa da ke gabar tekun Yemen, Sai dai ana zargin ‘kawancan saudiya dake kaddamar da hare-haren wuce gona da irin kan Al'ummar kasar ta Yemen da kai harin

A ranar Juma'ar da ta gabata aka bindige ‘yan gudun hijiran Somalia da suka hada da mata da kanana yara 42 a cikin wani jirgin ruwa da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai ta gabar tekun Yemen dake kalkashin ikon Gwamnatin kasar

Hukumar ‘yan gudun hijira ta Duniya ta ce akwai mutane akalla 80 da aka ceto bayan harin, inda 24 daga cikinsu ke cikin matsanancin hali.