Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Wasu 'Yan Ta'adda A Arewacin Kasar
(last modified Mon, 20 Mar 2017 10:43:22 GMT )
Mar 20, 2017 10:43 UTC
  • Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Wasu 'Yan Ta'adda A Arewacin Kasar

Jami'an tsaron kasar Masar sun sami nasarar kama wani adadi na 'yan wata kungiyar ta'addanci a kasar a lardin Sina' da ke arewacin kasar a ci gaba da fada da 'yan ta'adda da ake yi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya ba da rahoton cewa cikin wata sanawa da kakakin sojojin kasar Masar din Tamer al-Refaay ya fitar ya  bayyana jami'an tsaron sun sami nasarar kame wasu mutane 37 da ake zargi da aikata ayyukan ta'addanci rana guda bayan kisan gillan da aka yi wa wasu sojoji su 5 a garin al-Arish da ke lardin Sina.

Har ila yau kakakin sojin ya kara da cewa a wasu hare-hare da sojojin kasar suka kai  ta sama kan garuruwan Al-Arish da Sheikh Zawid da ke lardin Sina' din sun sami nasarar kashe wasu masu dauke da makami su 18.

Rahotanni dai sun ce a sabbin hare-haren da sojojin Masar din suke kai wa lardin na Sina' da yayi kaurin suna wajen ayyukan ta'addanci, tun daga farkon watan nan na Maris ya zuwa yanzu, sojojin sun sami nasarar kashe masu dauke da makami su 30 da kuma kame wasu 165.