Mutane da dama sun rasu sanadiyar fari a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18700-mutane_da_dama_sun_rasu_sanadiyar_fari_a_somaliya
Matsalar fari da kasar Somaliya ta fuskanta ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 26 cikin kwana guda kacal a wani yanki na kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:50+00:00 )
Mar 21, 2017 06:49 UTC
  • Mutane da dama sun rasu sanadiyar fari a Somaliya

Matsalar fari da kasar Somaliya ta fuskanta ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 26 cikin kwana guda kacal a wani yanki na kasar

Hukumar Telbijin da Radio na kasar Iran ya habarta cewa matsalar fari da kasar Somaliya ta fuskanta a shekarar Bana na ci gaba da kashe Mutane a kasar inda ciki kwana guda kacal  Mutane 26 suka rasa rayukansu a yankin Gobaland dake kalkashin ikon 'yan ta'addar kungiyar Ashabab a kudancin kasar.

Rahoton ya ce baga mutanan da suka rasa rayukansu,Duban Mutane sun yi hijra sanadiyar karamcin abinci a yankin, kuma a halin da ake ciki kimanin Mutane Milyan shida da dubu 200 ne ke bukatar taimakon gaggawa a kasar.

Ko baya ga kasar Somaliyan akwai kasashe da dama na yankin Afirka da suka fuskancin matsalar fari a shekarar ta Bana, lamarin da ya sanya Saktare Janar na MDD kira ga Shugabanin kasashen Afirka da su dauki mtakan gaggauta domin kalu balantar matsalar ta karamcin abinci.