Harin Bam ya hallaka Mutane 4 a Sanasanin 'yan gudun hijra
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18726-harin_bam_ya_hallaka_mutane_4_a_sanasanin_'yan_gudun_hijra
Wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a sansanin 'yan gudun hijra na arewa maso gabashin Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 22, 2017 07:54 UTC
  • Harin Bam ya hallaka Mutane 4 a Sanasanin 'yan gudun hijra

Wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a sansanin 'yan gudun hijra na arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya na cewa, a kalla mutum hudu ne suka mutu, yayin da wasu 18 kuma suka jikkata, sakamakon tashin bam a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin.

Tijjani Lumani daya daga cikin magabatan Sanasanin 'yan gudun Hijra na Muna ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Faransa cewa harin ya faru ne da misalin karfe 4.30 na asubahin wannan rana ta Laraba, kuma mafi yawa daga runfunar sansanin sun kone.

Sansanin 'yan gudun hijrar na Muna na dauke da duban 'yan gudun hijra da rikicin kungiyar Boko haram ya raba da mahalinsu.

Ko baya ga tashin tagwayen bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijrar, an tabbatar da tashin wani bam din a wata anguwa dake kusa da sansanin 'yan gudun hijrar ta Muna.