Jerin hare-haren ta'addanci a Najeriya
Wasu Mutane da ba a san ko su waye ba sun kai wasu jerin hare-haren ta'addanci a Jihar Benue dake kudu maso gabashin Najeriya.
A jiya Laraba, wasu mahara kan babura da Motoci sun kai harin ta'addanci a jihar Benue dake kudu maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar fararen hula akalla 20.
A ranar Litinin din da ta gabata ma wasu mahara sun kai hari a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum na jihar Benue, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Mutane akalla 31.
A safiyar Jiya Laraba an kai wasu tagwayen hare-haren ta'addanci a sansanin 'yan gudun hijra na Muna dake garin Maiduguri, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar 4 tare da jikkata wasu 18 na daban.
Baya ga rikicin Boko Haram Gwamnatin Najeriya na fuskantar fadace-fadacen kabilanci a wasu sassan kasar.