Jerin hare-haren ta'addanci a Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18754-jerin_hare_haren_ta'addanci_a_najeriya
Wasu Mutane da ba a san ko su waye ba sun kai wasu jerin hare-haren ta'addanci a Jihar Benue dake kudu maso gabashin Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 23, 2017 06:33 UTC
  • Jerin hare-haren ta'addanci a Najeriya

Wasu Mutane da ba a san ko su waye ba sun kai wasu jerin hare-haren ta'addanci a Jihar Benue dake kudu maso gabashin Najeriya.

A jiya Laraba, wasu mahara kan babura da Motoci sun kai  harin ta'addanci a jihar Benue dake kudu maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar fararen hula akalla 20.

A ranar Litinin din da ta gabata ma wasu mahara sun kai hari  a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum na jihar Benue, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Mutane akalla 31.

A safiyar Jiya Laraba an kai wasu tagwayen hare-haren ta'addanci a sansanin 'yan gudun hijra na Muna dake garin Maiduguri, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar 4 tare da jikkata wasu 18 na daban.

Baya ga rikicin Boko Haram Gwamnatin Najeriya na fuskantar fadace-fadacen kabilanci a wasu sassan kasar.