Lalubo hanyoyin magance rikicin siyasar kasar Sudan ta Kudu.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18758-lalubo_hanyoyin_magance_rikicin_siyasar_kasar_sudan_ta_kudu.
Mataimakin Sakatatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce lalubo hanyar Siyasa shi zai kawo karshen rikicin kasar Sudan ta Kudu.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 23, 2017 06:34 UTC
  • Lalubo hanyoyin magance rikicin siyasar kasar Sudan ta Kudu.

Mataimakin Sakatatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce lalubo hanyar Siyasa shi zai kawo karshen rikicin kasar Sudan ta Kudu.

Mista Hervé Ladsous  wakilin MDD a bangren Dakarun wanzar da zaman Lafiya na Majalisar a birnin Juba ya ce amfani da karfin Soja ba zai kawo karshen rikicin kasar ba, tattaunawa tsakanin bangarorin dake fada da juna ita ce hanya daya  cilo ta kawo karshen rikicin kasar.

A yayin da yake ishara kan ganawarsa da Shugaban kasar Sudan ta kudu,Mista  Ladsous ya bayyana cewa harakokin tsaro a kasar na cikin mawuyacin hali, da dama daga cikin Al'ummar kasar sun gudu sun ban gidajensu kuma wannan babban kalu bale ga Gwamnatin kasar.

Rikicin kasar Sudan ta kudu ya samo asali ne a watan Decambar 2013, shekaru biyu kacal bayan ballewar kasar da kasar Sudan.