Sudan Ta Kudu : Hukumomi Ne Umul-Aba'insin Yunwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18800-sudan_ta_kudu_hukumomi_ne_umul_aba'insin_yunwa
Masu sharhi kan lamuran yau da kulun sun dora alhakin bala'in yunwa dake shafar dariruwan al'umma a Sudan ta kudu kan mahukuntan kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Mar 24, 2017 17:58 UTC
  • Sudan ta kudu na daga cikin kasashen duniya da yunwa ke barazanawa al\\\\\\\'umma
    Sudan ta kudu na daga cikin kasashen duniya da yunwa ke barazanawa al\\\\\\\'umma

Masu sharhi kan lamuran yau da kulun sun dora alhakin bala'in yunwa dake shafar dariruwan al'umma a Sudan ta kudu kan mahukuntan kasar.

Ana ganin dai idan tallafin da ake badawa na ceto rayukan jama'a ya gaza, to fa ya kamata a duba hanyoyin samar da zamen lafiya mai daurewa domin kawo karshen ukubar da jama'ar wannan kasa ke ciki a cewar Alan Boswell wani mai sharhi kan al'amuran Sudan ta kudun.

Ya kara da cewa ba banza ne ba yankunan dake fama da yunwa a Sudan ta Kudun suka kasance a wani rahoto da MDD ta fitar inda kabilar Nuer na jagoran 'yan tawaye Riek Machar da kuma kabilar Dinka inda dakarun gwamnatin Salva Kiir keda iko.

Dama kafin hakadiyar Amurka a MDD, Michele Sison ta gargadi kwamitin tsaro na MDDn akan abubuwan dake kara dagula al'amuran magance yunwa a Sudan ta Kudu, musamen yadda bangarorin dake rikici a kasar ke kawo cikas wajen isar da kayan agaji ga mabukata.