Akalla Mitane 50 Sun Rasa Rayukansu A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18808-akalla_mitane_50_sun_rasa_rayukansu_a_jamhuriyar_afirka_ta_tsakiya
Sakamakon wani sabon rikici da ya sake ballewa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, akalla mutane 50 sun rasa rayukansu, wasu da dama kuma sun jikkata.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 25, 2017 02:14 UTC
  • Akalla Mitane 50 Sun Rasa Rayukansu A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Sakamakon wani sabon rikici da ya sake ballewa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, akalla mutane 50 sun rasa rayukansu, wasu da dama kuma sun jikkata.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoto daga birnin Bangui fadar mulkin jamhuriyar Afirka ta tsakiya cewa, tun daga ranar Talatar da ta gabata ce dai wasu masu dauke da makamai suka kai farmaki a  kan wasu ayyuka 3 da ke yankin Bambari a tsakiyar kasar.

Wasu daga al'ummomin yankin da suka tsere sun tabbatar da cewa, 'yan bindigar sun kashe mutane akalla 50 bisa ga abin da suka gani kafin su tsere, akwai yiwuwar adadin wadanda aka kashe ya zuwa yanzu ya haura hakan.

Mahukuntan kasar sun danganta abin da ke faruwa da wasu masu alaka da kungiyar Seleka, amma kungiyar ta nesanta kanta da abin da ke faruwa.