Gambiya za ta kafa Hukumar binciken Gwamnatin da ta shude
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18822-gambiya_za_ta_kafa_hukumar_binciken_gwamnatin_da_ta_shude
Gwamnatin kasar Gambia za ta kafa hukumar tabbatar da gaskiya da sasanta rikici wadda za ta gudanar da bincike kan barnar da aka tafka a lokacin gwamnatin Yahya Jammeh.
(last modified 2018-08-22T11:29:51+00:00 )
Mar 25, 2017 11:19 UTC
  • Gambiya za ta kafa Hukumar binciken Gwamnatin da ta shude

Gwamnatin kasar Gambia za ta kafa hukumar tabbatar da gaskiya da sasanta rikici wadda za ta gudanar da bincike kan barnar da aka tafka a lokacin gwamnatin Yahya Jammeh.

Ministan Shari’a na kasar Abubacarr Tambadou ya ce, hukumar za ta binciki dukiyar tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh da ya sha kaye a hannun Adama Barrow.Kazalika za a karfafa wa jama’a gwiwa don bada shedar miyagun ayyauakn da aka aikata a lokacin Jammeh, sannan kuma za a biya diyya ga wadanda aka ci zarafinsu.

Ana zargin tsohuwar gwamnatin da ta shafe shakaru 22 kan karagar milki  da azabtar da jama’a, abin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Kazalika ana zargin cewa, fiye da Dala miliyan 11 ya yi batan dabo daga asusun gwamnati bayan Jammeh ya fice daga kasar a cikin watan Janairun da ya gabata, wato bayan ya matsin matsin lambar mika mulki daga shugabannin Afrika