Masar: Mutane 3 Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Bom A Arewacin Kasar.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18826-masar_mutane_3_sun_mutu_sanadiyyar_tashin_bom_a_arewacin_kasar.
Majiyar tsaron Masar ta ce; Bom din dai ya tashi ne a garin al'arish,a yau asabar tare da kashe mutane 3 da kuma jikkata wasu shida.
(last modified 2018-08-22T11:29:51+00:00 )
Mar 25, 2017 18:16 UTC
  • Masar: Mutane 3 Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Bom  A Arewacin Kasar.

Majiyar tsaron Masar ta ce; Bom din dai ya tashi ne a garin al'arish,a yau asabar tare da kashe mutane 3 da kuma jikkata wasu shida.

Majiyar tsaron Masar ta ce; Bom din dai ya tashi ne a garin al'arish,a yau asabar tare da kashe mutane 3 da kuma jikkata wasu shida.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters da ya amabto majiyar tsaron ta Masar, ya kara da cewa; Bom din ya tashi ne dai akan hanyar da wata motar soja mai sulke ta ke wuce wa.

A ranar alhamis din da ta gabata ma dai an kashe wani jami'in dan sanda guda da kuma jami'in soja guda. 

A gefe daya, sojojin kasar Masar sun kashe 'yan ta'adda 15 a cikin yankin na al-arish.

Sojojin Kasar Masar dai suna fada da kungiyoyin daban-daban da su ke dauke da makamai a yankin Sinaa.