Shirin Mayar Da 'Yan Gudun Hijira Somaliya Na Nan Daram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18840-shirin_mayar_da_'yan_gudun_hijira_somaliya_na_nan_daram
Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya fada cewa shirin kasarsa na mayar da 'yan gudun hijira Somaliya dake tsugunne a sansanin Dadaab na nan daram, duk kuwa da matakin kotun kolin kasar na dakatar da shirin.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 26, 2017 01:13 UTC
  • Shirin Mayar Da 'Yan Gudun Hijira Somaliya Na Nan Daram

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya fada cewa shirin kasarsa na mayar da 'yan gudun hijira Somaliya dake tsugunne a sansanin Dadaab na nan daram, duk kuwa da matakin kotun kolin kasar na dakatar da shirin.

Shugaba Kenyatta ya fada a wani taron kungiyar kasashen yankin ta IGAD a birnin Nairobi cewa za'a ci gaba da mayar 'yan gudun hijirar.

Mista Kenyatta ya kare wannan matakin da cewa rashin kudi na nufin mutane na rayuwa cikin mawuyacin hali wanda zai iya cilasta masu aikata ayyukan ta'addanci.

A watan daya gabata ne kotun kolin kasar ta dakatar da shirin gwamnatin Kenyatta na korar 'yan gudun hijira Somaliya. 

Gwamnatin Kenya ta kuma mika kogon bara ga kasashen duniya akan su taimakawa sansanin na Dadaab dake karbar 'yan gudun hijira sama da kashi daya cikin hudu na al'ummar Somaliya.