Gunea Bissau: An Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Kin Jinin Shugaban Kasa
Dubban mutane a birnin Bissau sun yi Zanga-zangar kira ga shugaban kasa Jose Mario Vaz, da ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Dubban mutane a birnin Bissau sun yi Zanga-zangar kira ga hugaban kasa Jose Mario Vaz, da ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Fiye da shekara guda kenan dai Majalisar dokokin kasar ta Gunea Bissau ba ta yi zama ba, abinda ya kara fusata al'ummar kasar.
A ranar 11 ga watan nan na Maris ma dai daruruwan mutanen kasar sun yi gangami da Zanga-zangar kira ga shugaban kasar da ya yi bayani akan dalilin sauke pira minista Domingos Simoes Pereira daga kan mukaminsa.
A shekarar 2015 ne dai shugaban kasar ya sauke pira ministan daga kan mukaminsa. Tun bayan wancan lokacin an an nada wasu mutanen akan mukamin na Pira minista.