Yemen: Zanga-zangar Zagayowar Shekaru Biyu Da Shelanta Yakin Saudiyya.
Dubban mutanen kasar Yemen sun yi zanga-zanga a birnin Sanaa a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru biyu da fara harin Saudiyya a kasar.
Dubban mutanen kasar Yemen sun yi zanga-zanga a birnin Sanaa a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru biyu da fara harin Saudiyya a kasar.
Tashar telbijin din al-alam, mai watsa shirye-shiryenta da larabci daga nan Tehran, ta ambato babban sakataren kungiyar Ansarullah, Abdulmalik Badruddin al-Hutthy, yana cewa; Dubban mutanen kasar ta Yemen sun taro a filin Sab'in da ke birnin Sanaa, domin yin tir da hare-haren Saudiyya a kasar ta Yemen.
Ita kuwa tashar telbijin al-Masirah, ta Yemen, ta bada labarin cewa; Daga cikin mahalarta zanga-zangar da akwai shugaban kwamitinkoli ta siyasar Yemen, da shugaban majalisar wakilai da pira ministan.
A lokaci guda, babban sakataren kungiyar Ansarullah a Yemen,ya fitar da bayani akan cewa; Amerika da hramtacciyar Kasar Isra'ila da wasu kasashen duniya, sun shelanta yaki akan al'ummar musulmi. Har ila yau, ya ce; Washington ta shirya rusa al'ummar musulmi, kuma Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa suna taimakawa haramtacciyar kasar Isra'ila da kare manufofinta.