'Yan tawaye sun hallaka 'yan sanda 40 a D/Congo
Mahukuntan jihar Kassai a kasar D/Congo sun sanar da kisan 'yan sanda 40 daga 'yan tawaye bayan wani konton bauna da suka yi wa 'yan sandar.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Francois Kalamba Kakakin Gwamnan Jihar Kassai a jiya Assabar na cewa yan tawaye sun yi wa jami'an 'yan sanda kwantar bauna a yayin da suke hanyar garin Tashykapa zuwa Kananga, inda suka yiwa 40 daga cikin su yankan rago.
Rahoton ya ce 'yan tawaye sun bar 'yan sanda 6 daga cikin su saboda sun same su suna magana da yarar yankin.
A bangare guda Dakarun tsaron D/Congo sun sanar a jiya Assabar cewa sakamakon wani gumurzu tsakanin Sojojin kasar da 'yan tawaye a yankin Beni na gabashin kasar, soja guda tare da 'yan tawaye 3 sun rasa rayuakan su.
Sama da shekaru 20 kenan da kasar D/Congon ke fuskantar matsalar tsaro saboda kasancewar 'yan tawaye da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar.