Zazzabin Malariya Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Akalla 150 A Zimbabwe
Mar 27, 2017 17:34 UTC
Majiyoyin ma'aikatar kiwon lafiya a kasar Zimbabwe sun tabbatar da mutuwar mutane 151 sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin Harare fadar mulkin kasar ta Zimbabwe ya bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta ce, sakamakon ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a kasar a cikin 'yan kwanakin nan, hakan ya sanya an samu karuwar sauro, wanda ya jawo kamuwa da cutar Malariya.
Bayanin ya kara da cewa, kimanin mutane dubu 90 suka kamu da cutar a cikin 'yan lokutanan, amma mutum 151 suka rasa rayukansu, sauran kuma suna murmurewa bayan da suka karbi magani daga cibiyoyin kiwon lafiya na kasar.
Tags