Dubban Mutanen Kasar Sudan Ta Kudu Suna Hijira Zuwa Jamhuriyar DR Congo
Dubban mutane daga Kasar Sudan ta Kudu suna ci gaba da yin gudun hijira zuwa cikin kasar Dimokaradiyyar Congo saboda tashe-tashen hankula da suke ci gaba da yin kamari a yankunansu.
Kwamitin Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa: Dubban mutanen kasar Sudan ta Kudu mazauna yankunan jihar Equatoria ta Yamma suna ci gaba da yin gudun hijira zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da ke makobtaka ta su sakamakon barkewar tashe-tashen hankula a yankunansu.
Kwamitin Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Tashe-tashen hankulan da suke ci gaba da habaka a jihar ta Equatoria ta Yamma sun yi tsanani, inda ake bukatar hanzarta kai taimakon gaggawa musamman hanyoyin da za a bi wajen tsugunar da 'yan gudun hijiran, samar musu da abinci da magunguna.
Wani shaidan ganin ido a jihar ta Equatoria ta Yamma ya bayyana cewa; Matasa suna kai hare-haren wuce gona da iri kan mutane tare da wawushe dukiyoyinsu, aiwatar da kisan gilla, fyade ga mata tare da tilastawa yan mata aurensu.