Sabuwar Gwamnatin Somaliya Ta Ssamu Amincewar Majalisar Dokokin Kasar
Majalisar dokokin Somaliya ta amince da sabin Ministocin Gwamnatin Hasan Ali Khairi.
A jiya Laraba, Majalisar dokokin Somaliya ta amince da sabin Ministocin da Firaministan kasar Hasan Ali Khairi ya gabatar mata, inda daga cikin 'yan Majalisa 241 na kasar, 224 ne suka kada kuri'ar amincewa da sabbin Ministocin, 'yan Majalisa 15 suka kada kuri'ar kin amincewa, yayin da wasu biyu na daban suka kara farar kuri'a.
Bayan wannan ra'ayin amincewar da suka samu a Majalisar, sabin Ministocin za su yi rantsuwar kama aiki a gaban babbar kotun kasar,a farko wannan Wata da muke ciki ne Majalisar dokokin kasar Somaliyan ta amince da nadin da aka yiwa Hasan Ali Khairi a matsayin Firaministan kasar.
Wannan amincewa da Majalisar dokokin Somaliyan tayi na sabin Ministocin kasar na zuwa ne a yayin da kasar ke fuskantar babbar matsalar fari gami da hare-haren ta'addanci na kungiyar Ashabab.