Jagoran 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Ya Soki Kungiyar IGAD
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18988-jagoran_'yan_tawayen_sudan_ta_kudu_ya_soki_kungiyar_igad
Jagoran kungiyar 'yan tawayen kasar Sudan ta kudu Reick machar ya nuna rashin gamsuwarsa a kan matsayar da kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen gabashin Afirka IGAD ta dauka kan rikicin Sudan ta kudu.
(last modified 2018-08-22T11:29:53+00:00 )
Mar 31, 2017 06:41 UTC
  • Jagoran 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Ya Soki Kungiyar IGAD

Jagoran kungiyar 'yan tawayen kasar Sudan ta kudu Reick machar ya nuna rashin gamsuwarsa a kan matsayar da kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen gabashin Afirka IGAD ta dauka kan rikicin Sudan ta kudu.

Kmafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, jagoran 'yan tawayen Sudan ta kudu Reick Machar ya bayyana matsayar da kungiyar IGAD ta dauka kan rikicin Sudan ta kudu da cewa, shi ne babban abin yasa rikicin yaki ya ki cinyewa.

Machar ya ce bayan da aka cimma yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da bangaren gwamnati, kungiyar IGAD ba ta sanya ido kan yadda ake zartar da yarjejeniyar ba, bayan da ya amince ya koma Juba tare da karbar mukamin mataimakin shugaban kasa, domin kuwa a cewarsa gwamnatin Salva Kiir ta mayar da su saniyar ware kuma ta kudiri aniyar ganin bayansu, wanda hakan ne ya jawo rikicin ya ci gaba har zuwa yau.

A cikin makon da ya gabata ne shugabannin kasashen gabashin Afirka suka gudanar da zaman taronsu a birnin nairobi na kasar Kenya, inda suka bukaci 'yan tawayen Sudan ta kudu da su ajiye makamai, matakin da Machar ke kallonsa a matsayin rashin adalci gare su.