Najeriya : Adadin Mutanen Da Cutar Sankarau Ta Kashe Ya Kai 328
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19030-najeriya_adadin_mutanen_da_cutar_sankarau_ta_kashe_ya_kai_328
Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta sanar da cewa, cutar sankarau da ta bulla a kasar yau kusa da watani biyar ta yi sanadin mutuwar mutane 328.
(last modified 2018-08-22T06:59:54+00:00 )
Apr 01, 2017 06:44 UTC
  • Najeriya : Adadin Mutanen Da Cutar Sankarau Ta Kashe Ya Kai 328

Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta sanar da cewa, cutar sankarau da ta bulla a kasar yau kusa da watani biyar ta yi sanadin mutuwar mutane 328.

A sanarwar da ta fitar cikin daren jiya Juma'a ma'aikatar ta ce mutane 2,524 kawo yanzu suka kamu da cutar inda 328 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskia.

Annobar sabon nau'in cutar sankarau din dai ta shafi yankuna 90 a cikin jihohi 16 na kasar galibinsu kuma sun kasance a yankin arewa, sai kuma wasu yankuna a kudanci da suka hada da Osun, da Lagas da kuma Croos Rivers. 

Hukumomin lafiya na kasar dai sun ce suna daukan kwararen matakai na yaki da annobar, amma babbar matsalar dake akwai ita ce ta rashin isasun alluran riga kafin cutar.