Wasu 'yan bindiga sun kai hari a birnin Nairobi na kasar Kenya
Hukumar 'yan sandar Kenya ta sanar da kisan jami'inta guda tare da wasu fararen hula a wani harin da 'yan bindiga suka kai birnin Nairobi fadar milkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ta nakalto Hukumar 'yan sandar kenya na cewa a jiya Juma'a wasu 'yan bindiga sun kai hari a birnin Nairobi fadar milkin kasar inda suka kashe Akalla Mutane 9 daga cikin su har da Jami'in 'yan sanda guda.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko gungu da ya dauki alhakin kai hari, saidai ana zarkin kungiyar ta'addancin ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida da kai harin, ganin cewa kungiyar ta saba kai hare-haren ta'addanci a birnin na Nairobi da kuma wasu sassan kasar ta Kenya.
Har ila yau Hukumar 'yan sandar ta Kenya ta sanar da cewa Jami'anta sun cabke wasu Mutane uku dauke da makamai a Anguwar Pangami dake cikin birnin Nairobi inda ake zarkin su da hanu wajen kai harin , har ila yau wasu Jami'an 'yan sandar sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga a Anguwar Utawala dake cikin birnin na Nairobi tare da hallaka uku daga cikin su.