Shugabannin Wasu Kabilun Libya Sun Sanya Hannu A Kan Yarjejeniyar Sulhu
Manyan kabilun kudancin kasar Libya sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar sulhu a birnin Rom na kasar Italiya.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yau ma'aikatar harkokin cikin gida akasar Iraliya ta sanar da cewa, kabilun Tibu da kuma Aulad Sulaiman da ke kudancin kasar Libya, sun cimma matsaya a kan kawo karshen zaman doya da manja da suke yi, tare da rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu.
Bayanin ya ce an fara wannan tattaunawa tun ranar Juma'a da ta gabata, tare da halartar mutane 60 daga manyan dattijan kabilun biyu, da kuma wakilan gwamnatin Tripoli, gami da wakilan kabilun abzinawan Libya.
Dukkanin bangarorin dai za su yi aiki tare domin tabbatar da tsaro a kan iyakokin kudancin Libya, domin hana 'yan ci rani tsallaka iyakokin zuwa arewacin kasar domin tsallakawa zuwa turai, inda gwamnatin Italiya ta ce za ta ba su dukkanin taimakon da suke bukata domin gudanar da wannan aiki.