Wasu 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Kan Fararen Hula A Kasar Sudan
Wasu gungun 'yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi kan wata kasuwa da ke lardin Kordofan ta Arewa da ke kasar Sudan, inda suka kashe mutane tare da jikkata wani adadi na daban.
Shafin watsa labaran Al-Yaumus Sabi'i na kasar Masar ya habarta cewa: Wasu gungun mahara da suke cikin wasu tawagar motoci sun bude wuta kan jama'a a wata kasuwa da ke lardin Kordofan ta Arewa na kasar Sudan a jiya Lahadi, inda suka kashe mutane akalla bakwai tare da jikkata wani adadi na daban, sannan suka ari na kare.
Tun a shekara ta 2011 ne wani sabon gumurzu ya kunno kai tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da na 'yan tawayen kasar a yankunan da suke lardunan Kordofan ta Kudu da na Arewa gami da Blue Nile lamarin da ke ci gaba da lashe rayukan jama'a musamman fararen hula.