An Sake Gurfanar Da Shugaban Masu Gadin Sheikh Zakzaki A Gaban Kotu
A yau litinin ne jami'an tsaro a Nigeria suka sake gurfanar da shugaban masu tsaron Sheikh Ibrahim El-Zakzagi da abokan aikinsa biyu a gaban kotu tare da zargin cewa suna tallafawa ayyukan ta'addanci
Jami'an tsaron sun gabatar da Haruna Abbas, Ibrahim Musa da kuma Adam Sulaiman ne kan zargin aikinta laifuffuka guda 8 wadanda suka hada da zargin tallafawa ayyukan ta'addanci a tsakanin shekaru 2009-2013, har'ila yau da kuma tura yayan kungiyar Islamic Movement of Nigeria zuwa karban horon soje a Iran.
Zargin idan sun tabbata sun sabawa sashi na 4 na dokar hana ayyukan ta'addanci na shekara ta 2013. Alkalin kotun Justice Adeniyi Ademola na babban kotun tarayya a Abuja ya dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Mayu kuma ya bukaci a ci gaba da tsaresu a gidajen yari har zuwa lokacin.