Za A Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa A Kasar Gambiya.
Bayan kwashe shekaru 22, Al'ummar kasar Gambiya za su gudanar da zaben Wakilan su na Majalisar Dokokin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a ranar Alkhamis 6 ga watan Avrilu mai zuwa, Al'ummar kasar Gambiya za su gudanar da zaben 'yan Majalisar Dokoki, bayan da suka kwashe shekaru 22 bisa jagorancin milkin Shugaba Jammeh da bai basu damar gudanar da irin wannan zabe ba kalkashin inuwar Jam'iyun Siyasa.
Al'ummar kasar Gambiya dai na nuna adawar su kan dokokin da Shugaban kasar ya samar wanda ya samu amincewa daga Majalisar dokokin kasar ta ficin gadi.
A jiya Litinin ne aka kawo karshen rubuta suna na 'yan takarar wakilan Majalisar dokokin kasar, inda Mutane 239 da suka fito daga jam'iyun siyasa 9 suka rubuta sunan su.
Bisa kundin tsarin milkin kasar, kujeru 5 kacal ne daga cikin kujeru 53 na 'yan Majalisun ke kalkashin ikon Shugaban kasar, da a baya ya kasance kujeru 43.