Kungiyar Ashabab Ta Mamaye Wani Gari A Tsakiyar Kasar Somaliya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19138-kungiyar_ashabab_ta_mamaye_wani_gari_a_tsakiyar_kasar_somaliya.
Kungiyar Ashabab ta mamaye garin Elbur dake tsakiyar kasar Somaliya bayan ficewar Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka daga cikin garin.
(last modified 2018-08-22T11:29:55+00:00 )
Apr 05, 2017 05:34 UTC
  • Kungiyar Ashabab Ta Mamaye Wani Gari A Tsakiyar Kasar Somaliya.

Kungiyar Ashabab ta mamaye garin Elbur dake tsakiyar kasar Somaliya bayan ficewar Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka daga cikin garin.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Nur Hassan Gutale jami'in 'yan sanda a Jihar Galgudud ya ce a jiya Litinin Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka sun fice daga garin Elbur, lamarin da ya baiwa mayakan kungiyar Ashabab damar sake mamaye birnin.

Gutale ya zargi Dakarun kungiyar wanzar da zaman lafiya na AU da rashin sanin abin da zai biyo baya sanadiyar janyewar Dakarun da suka yi daga cikin garin na Elbur, kuma ya kara da cewa har yanzu sun kasa fahimtar dalilin da ya sanya Dakarun wanzar da zaman lafiyar na kasashen Afirka suka janye daga cikin garin na Elbur.

Kasar Somaliya dai ta kwashe shekaru da dama tana fuskantar matsalar mamayar kungiyar 'yan ta'adda na Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida, a watan Augustan shekarar 2011 Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka tare da Dakarun kasar Somaliya sun samu nasarar fitar da mayakan Ashabab din daga Magadishu babban birnin kasar. kuma har ya zuwa yanzu mayakan na Ashaban na rike da wasu kauyukan kasar.