A Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa A Kasar Gambia
Apr 06, 2017 12:29 UTC
A yau ne ake gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar Gambia, a matsayin zaben 'yan majalisar dokoki na farko bayan kayar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.
Hukumar zaben kasar Gambia ta sanar da cewa, tun kimanin karfe 8 na safiyar yau ne aka bude akwatunan zabe a fadin kasar ta Gambia, kuma za a ci gaba da kada kuri'a har zuwa karfe 5 na yammacin yau.
Mutane dubu 886 ne a kasar Gambia suka cancanci kada kuri'a a kasar, inda za su zabi 'yan majalisar 53 daga cikin kujeru 58 na majalisar, inda shugaban kasa yake da kujeru 5 a majalisar, sabanin lokacin mulkin Yahya Jammeh, inda yake da hakkin kujeru 43 daga cikin kujeru 58 na majalisar.
Tags