Gwamnati Kasar Masar Ta Karbi Jiragen Yaki Samfurin Rafale Kirar Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19184-gwamnati_kasar_masar_ta_karbi_jiragen_yaki_samfurin_rafale_kirar_kasar_faransa
Gwamnatin kasar Masar ta bada sanarwan karban jiragen yaki samfurin Rafale kirrar kasar Faransa guda ukku a jiya Laraba.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Apr 06, 2017 11:58 UTC
  • Gwamnati Kasar Masar Ta Karbi Jiragen Yaki Samfurin Rafale Kirar Kasar Faransa

Gwamnatin kasar Masar ta bada sanarwan karban jiragen yaki samfurin Rafale kirrar kasar Faransa guda ukku a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labaran Skynews ya nakalto majiyar sojojin kasar Masar ta na bayyana haka a wani rahoton da ta fitar a jiya Laraba. Rahoton ya kara da cewa kafin jiyan sojojin sama na kasar ta Masar sun karbi jiragen yaki samfurin na Rafale guda 6 daga kasar Faransa, wanda idan an hada da wadanda suka karba jiya zasu tashi zuwa jirage  9 kenan.

A cikin watan Jenerun shekara ta 2015 ne  gwamnatin kasar Masar ta kulla yerjejeniyar sayan jiragen yaki 24 daga kasar Faransa don bunkasa ayyukan rundunar sojojin saman kasar, musamman don fuskantar yan ta'adda a yankin Sinaa daga arewacin kasar.