An Gurfanar Da Tsohuwar Ministan Man Fetur Na Nigeria A Gaban Kotu
An shigar da karar tsohuwar ministan man fetur na Nigeria a gaban wata babbar kotu a Abuja kan zargin bada cin hanci na Naira million 264 ($1.4) a zaben shugaban kasa na shekara ta 2015.
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Diezani Allison-Madueke ta bada naira miliyon 246 ga ma'aikatan hukumar zabe (INEC) guda ukku don tallafawa tsohun shugaban kasar Goodluck Jonathan lashe zaben shugaban kasa na shekara ta 2015.
Allison-Madueke dai, yar shekara 56 a duniya ba ta cikin kotun a lokacinda mai gabatar da karan yake karanta tuhume tuhumen da ake mata. Mai gabatar da kara na hukumar EFCC Rotimi Oyedepo ya ce alkali Mohammad Idris ya bada belin ma'aikatan hukumar zaben da suka karsbi kudaden guda biyu, wato -Yisa Olarenwaju da Tijani Bashir, - kan kudade nai milllion 50, sanna na ukkunsu Christian Nwosu ya mikawa hukumar ta EFCC kadarori masu kimar naira milion 25 da kuma kudade naira milion 5.
A lokacin mulkin tsahon shugaban kasar ne bambam bankin kasar ta bada sanarwan bacewar dala biilion $20 daga asusun man fetur na kasar wanda Allison-Madueke ke kula da shi.