ICC Za Ta Saurari Afrika Ta Kudu Kan Kin cafke Al-Bashir
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19206-icc_za_ta_saurari_afrika_ta_kudu_kan_kin_cafke_al_bashir
Yau Juma'a ne ake sa ran kotun hukunta mayan laifuka ta duniya za ta saurari gwamnatin Afrika ta Kudu kan kin cafke shugaba Omar Al-Bashir na Sudan da take zargi da laifin kisan kare dangi.
(last modified 2018-08-22T06:59:55+00:00 )
Apr 07, 2017 00:05 UTC
  • ICC Za Ta Saurari Afrika Ta Kudu Kan Kin cafke Al-Bashir

Yau Juma'a ne ake sa ran kotun hukunta mayan laifuka ta duniya za ta saurari gwamnatin Afrika ta Kudu kan kin cafke shugaba Omar Al-Bashir na Sudan da take zargi da laifin kisan kare dangi.

A wannan zamen, kotun ta ICC za ta duba ko Afrika ta Kudun a matsayinta na mamba ta gaza sauke nauyin daya rataya akan ta na cafke Al-bashir ne domin mika mata shi ko kuma A'a.

A watan Yuni shekara 2015 ne Al-bashir ya sanya kafa a kasar ta Afrika ta kudu a yayin taron kungiyar tarayya Afrika a Johannesburg, inda kotun ta ICC ta bukaci a cafke mata shi, saidai ya sulale ba tare da mahukuntan Afrika ta Kudun sun yi hakan ba.

Kotun ICC dai ta jima tana neman shugaba Al'Bashir ruwa a jallo, kuma kayo yanzu ta fitar da sammacin kasa kasa na neman kame shi har sau biyu bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama da kisan jama'a a yankin Darfur.

Shugaba Al'Bashir wanda ke musunta duk wadanan zarge-zargen na ci gaba da jan ragamar mulkin wannan kasa tare da tafiye-tafiyesansa musamen a nahiyar ba tare ya nuna ma damuwa ba.

A kwanan baya dai Afrika ta Kudu ta yi barazanar ficewa daga kotun ta ICC saboda wannan kace-nace, aman wata kotun kasar ta ki amuncewa da hakan.