Mutuwar Hassan al-Turabi Na Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1921-mutuwar_hassan_al_turabi_na_sudan
Dr. Hassan al-Turaby Na Sudan ya Rasu Yana Dan Shekaru 84
(last modified 2018-08-22T06:57:56+00:00 )
Mar 05, 2016 16:12 UTC
  • Mutuwar Hassan al-Turabi Na Sudan

Dr. Hassan al-Turaby Na Sudan ya Rasu Yana Dan Shekaru 84

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya nakalto cewa; Allah ya yi wa dan hamayyar siyasar kasar Sudan Hassan al-turaby rasuwa da safiyar yau asabar.

Rahotanni daga birnin Kahrtum sun ambaci cewa; Turaby wanda ya ke da shekaru 84 ya kamu da bugun zuciya ne da safiyar yau asabar abinda ya sa aka kai shi asibitin Royal da ke birnin Khartum. Ya rasu bayan wani lokaci da kai shi asibitin.

Gabanin Rasuwarsa Hassan al-Turaby ya kasance dan siyasa mafi shahara a kasar sudan a cikin shekarun bayan nan.