Shugaban Somaliya Ya Sha Alwashin Yaki Da Al'Shabab
Shugaban kasar Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed, yashelanta yaki kan kungiyar Al-Shabaab tare da aiwatar da sauye sauye a bangaren harkar tsaro na kasar dake fuskantar barazanar kungiyar ta Al'Shabab.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani harin tagwayen bam da ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da raunata wasu 10.
Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed ya nada tsohon jakadan kasar a Birtaniya Mohammed Ali Sanbaloolshe, a matsayin shugaban hukumar leken asiri, yayin da ya nada Jimale Irfid a matsayin sabon babban hafsan tsaro na kasar.
Shugaban kasar ya kuma dawo da tsohon shugaban rundunar 'yan sandan kasar, Abdihakim Dahir kan mukaminsa, inda ya kuma nada mataimakin jakadan kasar a Amurka, Thabit Mohammed Abdi matsayin magajin garin Mogadishu, kuma gwamnan yankin Banadir.
Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed ya shaidawa manema labarai a Mogadishu cewa, kasar ta kaddamar da yaki a kan mayakan Al-Shabaab, yana mai cewa, gwamanti ta ba su kwanaki 60 su mika wuya ita kuwa ta kyautata musu rayuwa.