An Kai Harin Rokoki A Babban Birnin Kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19224-an_kai_harin_rokoki_a_babban_birnin_kasar_somaliya
Majiyar tsaron Somaliya ta sanar da mutuwar Mutane 3 sanadiyar harin rokoki da aka kai fadar milkin kasar
(last modified 2018-08-22T11:29:56+00:00 )
Apr 07, 2017 18:04 UTC
  • An Kai Harin Rokoki A Babban Birnin Kasar Somaliya

Majiyar tsaron Somaliya ta sanar da mutuwar Mutane 3 sanadiyar harin rokoki da aka kai fadar milkin kasar

Majiyar ta sanar da cewa harin rokokin da aka kai a wannan Juma'a kusa da wurin bincike na filin sauka da tashi na jirgin saman birnin Magadushu .ya hallaka Mata uku na iyali guda.

A ranar Larabar da ta gabata ma, an kai wani harin ta'addanci a wani wurin cin abinci dake kusa da Ma'aikatar tsaron kasar, lamarin da ya yi sanadiyar fararen hula akalla 7.

A jiya Alhamis ne Shugaban kasar Mohamed Abdullahi ya sauya manyan hafsoshin tsaro, ya kuma yi kiran mayakan Al Shabab da su yi saranda cikin kwanaki 60. Tuni ma jami'an 'yan sandan Somaliya suka dora alhakin harin kan mayakan Al Shabbab.

Sai dai ba a sami martanin Al Shabbab din da ake zargi ba, amma a baya ta sha daukar alhakin irin wadannan hare hare a kasar.