Gargadin Ga 'Yan tawayen Kasar Gunea Bissau
Mar 05, 2016 16:14 UTC
Gwamnatin Gunea Bissau Ta Gargadin 'Yan tawayen Kasarta.
Babban kwmandan Sojan Kasar Gunea Bissau Janar Big Natam ya ja kunnen 'yan tawayen kasar.
Kwamandan Rundunar Sojojin Kasar ta Gunea Bissau ya fadawa 'yan tawayen kasar da su dawo rakiyar kitsawa kasa da al'umma makarkashiya, idan kuwa ba haka ba, sakamakonsu kisa.
Big Natam ya kara da cewa; Nauyin da ya rataya a wuyan soja shi ne tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro, saboda da haka a duk inda wata makarkashiya ta kunno kai za su murkusheta tun tana karama.
Shekaru biyu kenan a jere kasar ta Gunea Bissau tana a karkashin gwamnatin rikon kwarya wacce ta ke samun kariya daga soja.
Tags